Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

Zargin aikata lalata da mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana binciken wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar su uku da ake zargi da yin lalata da mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, mako daya bayan da shugaban ofishin Majalisar ta Minusca Babacar Gaye ya yi marabus daga mukaminsa saboda wani zargin makamancin wannan.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Bangui.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Bangui. AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Bayanai dai sun ce lamarin ya faru ne a garin Bambari da ke arewa maso gabashin kasar, kuma sojojin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ne ke aikin wanzar da zaman lafiya a can.

A yanzu dai ana sauraren MDD ta sanar da irin matakin da take shirin dauka dangane da wadanda ke da hannu a wannan lamari da ke iya shafa wa ayyukanta a sauran sassan duniya kashin kaji.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.