An dan samu lafawar tashin hankali a Bangui na kasar Afrika ta tsakkiya
A jiya Assabar a dan samu lafawar tashin hankali a birnin Bangui babban birnin Jamhuriya Afrika ta Tsakkiya, bayan taho mugamar tsawon kwanaki 4 da aka share ana yi a birnin,
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yanzu haka dai shugabar gwamnatin rikon kwaryar kasar Uwargida Katrin Samba Panza na ta fafatukar tattaunawa da shuwagabannin kungiyar mayakan sa kai Kristoci makiya musulunci da musulmi a kasar (Anti Balaka), da nufin samar da kwanciyar hankali mai dorewa a wannan kasa.
Tashin hankalin da ya wakana dai shine irinsa mafi muni da aka gani tun karshen watan Ogustan da ya gabata a birnin na Bangui, wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 10, da suka hada da wani sojan samar da zaman lafiya na Majalisar DD dan kasar Pakistan guda, da aka kashe a ranar alhami, a yayin da wasu da dama daga cikin dakarun na duniya suka samu raunuka
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu