Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Yan tawayen Afrika ta Tsakiya sun yi bore a Bangui

Tsoffin ‘yan tawaye musulmi a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, wadanda aka kwancewa damara sannan aka tara su a wani barikin soja da ke birnin Bangui, sun gudanar da zanga-zangar a jiya Alhamis.Tsoffin ‘yan tawaye musulmi sun nuna adawa da shirin hukumomin kasar na mayar da su yankunansu na asali.

Wasu masu zanga zangar a birni Bangui
Wasu masu zanga zangar a birni Bangui © Pierre Terdjman Exposition produite par Paris Match
Talla

Sun dai wadannan tsoffin ‘yan tawaye magoya bayan kungiyar Seleka, wadda ta kori shugaban Francois Bozize daga karagar mulki a farkon shekara ta 2013, an soma tattara su a cikin barikin sojan ne a farkon wannan shekara a karkashin shirin samar da zaman lalfiya a kasar.
A sanyin safiyar jiya alhamis ne dai suka soma gudanar da wannan zanga-zanga, wasu daga cikinsu dauke da makamai yayin da wasu ba sa dauke da makamansu, kuma sun ja daga a kofar barikin sojan da aka tattara su domin nuna fushinsu.
An gudanar da tarzomar ne a gaban idon dakarun Majalisar dimkin duniya da kuma na Faransa.
Mazauna birnin Bangui dai sun yi matukar razana a lokacin da suka samu labarin cewa tsoffin ‘yan tawayen sun tayar da bore a cikin wannan bariki, musamman ma lura da yadda ake ci gaba da samun tashe tashen hankula a cikin birnin da kuma sauran yankunan kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.