Bangarori masu hamayya da juna a Libya na taro a Maroko
Bangarori masu hamayya da juna a rikicin kasar Libya na gudanar da taro a wannan litinin a kasar Maroko a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya a yunkurin da ake na samar da mafita ga rikcin da ake fama da shi tun bayar kawar Muammar Kaddafi daga karagar mulki.
Wallafawa ranar:
Manzon musamman na MDD a kasar ta Libya Bernardino Leon na kokarin samar da yarjejeniya ne a tsakanin bangarorin kafin ranar 17 ga wannan wata da ake shirin fara azumin watan Ramadana.
Yanzu haka dai kasar ta Libya akwai gwamnatoci biyu, majalisun dokokin biyu masu hamayya da juna, yayin da sauran kungiyoyin ‘yan bindiga cikinsu har da magoya bayan Alqaida ke ci gaba da yin iko da wasu yankunan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu