Isa ga babban shafi
Nijar

An yi zanga-zangar adawa da gwamnati a Nijar

A birnin Yamai na jamhuriyar dubban mutane ne suka shiga zanga-zangar lumana a ranar asabar, inda suke nuna adawarsu dangane da irin matsalolin da suka ce kasar na fuskanta, da suka hada da yadda gwamnati ke tafiyar da yaki da Boko Haram, karancin wutar lantarki da kuma tursasasawa shugabannin kungiyoyin fararen hula. 

Masu zanga-zangar lumana a Yamai jamhuriyar Nijar
Masu zanga-zangar lumana a Yamai jamhuriyar Nijar AFP/Boureima Hama
Talla

Har ila yau masu zanga-zangar sun bukaci a kwace tafiyar da aikin fitar da kaya da aka bai wa wani kamfanin kasar Faransa mai suna Bollore, aikin da a can baya ma’aikatan Kostum ko Duwan ke yi, da kuma kawo gyra a game da yadda ake tafiyar da aikin hako Uranium a kasar.

To sai dai hukumomi a kasar ta Nijar sun bayyana cewa wadanda suka shiga zanga-zangar ta jiya ba wasu ba ne face magoya bayan jam’iyyun adawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.