Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza ya kore Ministoci uku

A yau litinin sabuwar zanga-zanga ta sake barkewa tsakanin al'ummar kasar Burundi masu adawa da matakin Shugaba Pierre Nkurunziza na sake tsayawa takara a babban birnin kasar na Bujumbura.Lamarin da ke zuwa adai-dai lokacin da Fadar shugaban kasar ta sanar da korar wasu manyan ministoci kasar cikinsu hadda na tsaro.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza RFI / SR
Talla

Tun daga safiyyar yau litinin, wasu al’ummar kasar suka sake kaddamar da sabon gangami a birnin Bujumbura, tare da raye-raye da busa wusar, yayyin da sojojin kasar ke fatatakar su da harbe-harbe a sama, kwanaki kalilan bayan murkushe kokarin juyin mulki a kasar, duk da dai gwamnati ta yi gargadi akan zanga-zangar.

Jami’an da ke kokarin tarwatsa masu zanga-zangar na musu barazanar bude wuta, in dai basu bar kura ta lafa ba.

A halin yanzu dai rahotannin daga fadar gwamnatin kasar na cewa, Nkurunziza, ya kore manyan ministoci 3 a gwamnatinsa, wadanda suka hadda da minista tsaro, da na harkokin waje da na kasuwanci, kuma tuni aka zabe wadanda za su maye gurbinsu.

Rikicin siyasar Burundi dai tayi ajali mutane akalla 20, wadanda ke bore kin jini kudurin Nkurunziza, kafin kokarin kaddamar da juyin mulki kasar da bai samu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.