Isa ga babban shafi
Burundi

Akwai Yiwuwar jinkirta zabe a Burundi

A kasar Burundi akwai yiyuwar a jinkirta gudanar da zaben shugabancin kasar da ma na ‘yan majalisa wadanda aka tsara gudanarwa a cikin watanin Mayu da Yuni masu zuwa. Wannan dai ya biyo bayan yunkurin Juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba da kuma sauran abubuwa da suka biyo baya. 

Shugaban Burundi da Sojoji suka yi yunkurin hambararwa ya samu tarbe daga Magoya bayan shi a Bujumbura
Shugaban Burundi da Sojoji suka yi yunkurin hambararwa ya samu tarbe daga Magoya bayan shi a Bujumbura REUTERS
Talla

Wani na hanu daman shugaban Burundi, Willy Nyamitwe, yace al’amura da suka faru a kasar hujja ce da hukumar zaben kasar za ta iya amfani dasu wajen jinkirta zaben kasar.
A jiya lahadi ne, Shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana a karon farko tun bayan yunkurin juyin mulkin kasar na makon da ya gabata.

Shugaban da ke murmushi a lokacin da ya ke hira da manema labarai a fadar shi da ke birnin Bujumbura, ya ki cewa komai akan rikicin siyasar kasar
Sai dai ya ce ya dawo kuma zai cigaba da jan ragamar mulki a matsayinsa na shugaban kasar burundi tare da magana akan barazanar da kasar ke fuskanta daga kungiyar al-shabab na somalia.

Nkurunziza dai ya fuskanci kalubale da dama daga al’ummar kasar, wanda ke nuna adawa da matakin sake tsayawa takara a wani wa ‘adi na 3 .
A yanzu dai dakarun gwamnati Nkurunziza na cigaba farautar cafke masu yunkurin juyin mulkin a kasar.
Duk da a yanzu akwai wasu mutane 17 a hannu dake da za su fuskantar shari ‘a .

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.