Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta kudu na fuskantar matsin lamba

Kungiyoyi kare hakkin bil'adama a Duniya tare da wasu manyan kasashe na ci gaba da yin matsin lamba ga bangarorin da ke rikici a kasar Sudan ta kudu akan su kawo karshen yakin basasan da aka kwashe sama da shekara guda ana yi yanzu haka.

Sojojin Sudan ta kudu da ke fada da dakarun Riek Machar tsohon mataimakin shugaban kasa
Sojojin Sudan ta kudu da ke fada da dakarun Riek Machar tsohon mataimakin shugaban kasa AFP PHOTO/Charles LOMODONG
Talla

Yunkurin kasashen da ke gabacin Afirka na magance rikicin Sudan ta kudu ya ci tura tun ballewar mataiamakin shugaban kasar Riek Machar wanda aka kora daga mukaminsa.

Yanzu haka ana saran kungiyar kasashen Afirka da Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Amurka da China su jagoranci wani yunkuri da ake saran zai kawo karshen tashin hankalin a kasar.

Daruruwan mutane suka mutu a Sudan ta kudu a rikicin kasar tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.