Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Ban Ki-moon ya ja kunnen Shugabannin Sudan ta Kudu

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir da kuma jagoran ‘yan tawayen kasar Riek Machar da su bi sannu kuma su yi la’akari da rayukan bayin Allah a ci gaba da yakin da suke yi a kasar.

Riek Machar da Salva Kiir a birnin Addis Ababa
Riek Machar da Salva Kiir a birnin Addis Ababa REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Ban ya yi kira ga bangarorin biyu su cire son zuciya domin tabbatar da zaman lafiya a kasar da suka jefa cikin matsanancin hali.

Bangarorin biyu sun sanya hannu cikin wata yarjejeniyar aiki tare da juna domin kawo karshen tashin hankalin da ake samu a kasar, amma ba tare da amincewa da bukatar kafa gwamnatin hadaka ba.

Ban Ki-moon ya nuna damuwa kan yadda aka dauki lokaci bangaorirn biyu ba su amince da juna ba game da tsarin zaman lafiya.

Dubban mutanen kasar Sudan ta kudu ne aka kashe tare da jefa miliyoya cikin matsanancin hali na yunwa sakamakon rikici tsakanin Shugaban kasar Salva Kiir da tsahon mataimakinsa Riek Machar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.