Ana cigaba da barin wuta a Sudan ta Kudu
YAN tawayen Sudan ta kudu sun ce yanzu haka ana ci gaba da barin wuta a arewacin kasar tsakanin mayakan su da sojojin gwamnati
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun yan tawayen Lony Ngundeng, ya zargi sojojin gwamnati ne da kaddamar da hari akan su, inda yace sun samu nasarar yi musu mummunar illa.
To saidai babu wata majiya ta dabam da ta tababtar da labarin.
a watan Disamban shekara ta 2013 ne, yakin basasa ya fara a kasar, bayan shugaba Salva Kirr ya zargi Riek Machar da yin kokarin kifar da gwamantinsa
yakin dai, yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama, bayaga kusan miliyan uku da suka kauracewa gidajensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu