Masu adawa a da juna a Sudan ta Kudu za su cimma yarjejeniya
Masu adawa tare da yaki da juna a kasar sudan ta Kudu, sun yi shirin gudanar da wata sabuwar yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakaninsu. yayinda masu sasantawa na Gwamnati, suka bayyana yakinin cewa, za’a samu yarjejeniya mai daurewa tsakanin bangarorin biyu, duk da cewa fada na cigaba da kaurewa tsakaninsu
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A cewar ministan ‘yada labarai na kasar, kuma jagoran wakilan gwamnati a tattaunawar, Michael Makuei, “mu na da yakinin samar da yarjejeniyar tsagaita buda wuta tsakanin bangarorin kuma zamu halarci taron ne, da nufin maidowa al-ummar Sudan ta Kudu zaman lafiya”.
Makuei, ya shaidawa manema labarai haka ne, a lokacin da ya ke dab da tafiya birnin Addis Ababa na Ethiopia, inda za’a gudanar da tattaunawar.
Tuni dai wakilan ‘yan tawayen suka isa Kasar ta Ethiopia domin tattaunawar, yayinda sau bakwai kenan da suka warware yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu