Isa ga babban shafi
Nijar-Chadi

Dakarun Nijar da Chadi sun kori Boko Haram a gabar tabkin Chadi

Dakarun kasar Nijar da Chadi sun kai wa Boko Haram farmaki a gabar tabkin Chadi inda mayakan na Najeriya suka kafa sansani, Sojojin sun fatattaki mayakan, kamar yadda wata majiyar tsaron Nijar ta tabbatar wa Kamfanin dillacin labaran Reuters.

Ayarin dakarun Chadi da ke fada da Mayakan Boko Haram na Najeriya
Ayarin dakarun Chadi da ke fada da Mayakan Boko Haram na Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Wata majiyar tsaron tace mayakan Boko Haram da dama ne aka kashe a hare haren kasa da sama da aka kai wa sansaninsu.

Majiyoyin sun ce babu hannun dakarun Najeriya a farmakin da aka kai wa Boko Haram.

Wani Jami’in tsaron kasar Chadi ya ce kimanin ‘yan Boko Haram 50 aka kashe a farmakin, amma Sojojin Chadi biyu sun mutu a harin da suka kai a kusa da garin Abalam a ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce dakarun Nijar da Chadi sun doshi garin Malam Fatori da ke kan iyaka tsakanin Nijar da Najeriya.

Tuni dai dakarun Nijar da Chadi da Kamaru suka fatattaki Boko Haram a garuruwan da suka kwace a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.