Isa ga babban shafi

Zabe zai taimaka wajen kawar da Bokoharam a Najeriya-Obama

A wani sako ta faifan bidiyo da ya aikewa al’ummar Najeriya a yau litinin, shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci al’ummar kasar da su fito su yi zabe a ranar asabar mai zuwa ba tare da tashin hankali ba

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama Reuters/路透社
Talla

Obama ya ce ‘yan Najeriya na da damar yin zabe a cikin kwanciyar hankali ba tare da tursasawa ba, inda shugaban na Amurka ya bayyana zaben a matsayin mai muhimmanci lura da matsayin Najeriya ta fannin yawan al’umma da kuma karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Shugaban na Amurka ya bayyana zaben a matsayin wata dama ga ‘yan Najeriya domin kawo karshen ayyukan Boko Haram da suka yi sanadiyyar mutuwar dimbin mutane a kasar.

A ranar 28 ga watan Maris dina da kuma 11 ga watan Afrilu mai zuwa ake saran al'umma kasar su fita domin kada kuri'un su

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.