Isa ga babban shafi
Najeriya

Dakarun Chadi da Nijar sun kori Boko Haram a Gachagar

Sojojin Nijar da Chadi sun kwace ikon garin Gachagar bayan sun kori mayakan kungiyar Boko Haram daga garin inda suka mamaye na wani dogon lokaci. Rahotanni sun ce sojojin da suka kubutar da garin Damasak ne suka kama Gachagar bayan wani hari da suka kai jiya da safe.

Sojin Nijar da ke fada da Boko Haram na Najeriya
Sojin Nijar da ke fada da Boko Haram na Najeriya REUTERS/Joe Penney
Talla

Wakilin kamfanin Dillan Labaran Reuters a Diffa ya ce sun ji karar fashe fashen makamai lokacin da sojojin suka shiga kauyen.

Ministan tsaron Nijar Mahamadou Karidjo ya ce an kai wa mayakan Boko Haram hare hare ne ta sama da kasa, kuma yanzu dakarun Nijar da Chadi za su doshi garin Malam Fatori wanda ke kusa da kan iyaka da Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.