Isa ga babban shafi
Sudan

Mutum Dubu 41 sun bar gidajensu a yankin Darfur na Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fada tsakanin dakarun gwamnati da yan tawaye a yankin Darfur na kasar Sudan ya tilastawa mutane akalla dubu 41 tserewa daga gidajensu kama daga watan Disamban Baara

RFI Hausa
Talla

Sanarwar da Majalisar dunkin Duniya ta fitar dai na zuwa ne bayan wani zaman tattaunawa tsakanin majalisar da hukumomin kungiyar tarayyar Afruka a Khartoum na kasar ta Sudan, kan batun ficewar Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen yammaci daga kasar.

Majalisar dinkin Duniyar dai na cewa akwai yiyuwar yawan wadanda suka tserewa rikicin, ya haura adaddin da suka fitar sakamakon yadda kididigar da aka gudanar daga watan Disamban Baara zuwa wannan makon na Febrairu ke nunawa.

Daga farkon rikicin sudan rahotannin hukumar na bayyana cewar sama da mutane dubu 300 ne suka rasa rayukansu yayin da kuma sama da miliyan 2 suka bata.
Dakarun gwamnatin Sudan sun kaddamar da hare hare a yankin Darfur da zummar murkushe ‘yan tawayen da suka dade suna fafatawa da gwamnati tun shekara ta 2003.

Sai dai mai Magana da Yawun Rundunar sojin kasar kanal Al-sawarmy Khaled, ya musanta wannan alkalumma, inda ya shaidawa kamfanin dilanci labaran faransa na AFP cewa yanzu kusan wata guda kenan rabansu da kaddamar da hare a yankin Darfur sai dai idan alkaluma rikicin baya ne aka fitar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.