Isa ga babban shafi
Sudan

'Yan tawayen Sudan sun kame ma'aiktan agaji 'yan kasar Bulgaria

Yau Laraba ‘Yan tawayen kasar Sudan ta Kudu sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasar Bulgaria 6, dake aiki da Majalisar Dinkin Duniya. Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace, ‘Yan tawayen sun kame mutanen ne, bayan da suka tilasta wa jirgin sama mai saukar Ungulu da mutanen ke ciki ya sauka. Jirgin mai dauke da alamar Majalisar Dinkin Duniya, ya taso ne daga kasar ta Sudan ta Kudu, inda ya nufi Khartoum babban birnin kasar Sudan, inda yayi saukar gaggawa a yankin Kordofan, na kasar ta Sudan.Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Bulgaria tace, yanzu haka mutane 6 suna hannun ‘yan kungiyar SPLM-N, dake yaki da hukumomin birnin Khartoum, tun lokacin da Sudan ta Kudu ta balle daga kasar, cikin shekarar 2011.Har yanzu ba a san hakikanin dalilin sauko da jirgin saman ba, amma hukumomin na Bulgaria sun ce suna kokarin ganin an sako mutanen cikin gaggawa.Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Jane Howar, tace suna da yakinin cewa mutanen suna cikin koshin lafiya.Hower ta kara da cewa bata ga dalilin da za a kame mutanen ba, ganin cewa suna aiki agaji ne. 

Wani dan kungiyar SPLM, yana zaune a shingen da suka yi a yankin Kordofan
Wani dan kungiyar SPLM, yana zaune a shingen da suka yi a yankin Kordofan Reuters/Zohra Bensemra
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.