Isa ga babban shafi
Madagascar

An rusa gwamnatin Madagascar

Shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina ya rusa gwamnatin kasar saboda gazawar gwamnati wajen shawo kan matsalar wutar lantarki da al’ummar ke fama da ita. Shugaban yace tsohuwar gwamnatin za ta ci gaba da tafiyar da kasar kafin nada sabuwa.

Hery Rajaonarimampianina, na Madagascar
Hery Rajaonarimampianina, na Madagascar AFP PHOTO/RIJASOLO
Talla

Shugaba Rajaonarimampianina ya bayar da sanarwar rusa gwamnatin ne a cikin daren Litinin ba tare da bayyana dalili ba.

Amma gwamnatin Firaminista Roger Kolo na fuskantar kalubalen magance matsalar wutar lantarki a kasar, al’amarin da ya sa mutanen kasar suka fito saman titi suna zanga-zanga.

Tuni dai gwamnatin kasar ta kori Ministan makamashi saboda gazawarsa wajen magance matsalar.

A watan Afrilun shekarar 2014 ne Rajaonarimampianina ya nada Kolo a matsayin Firimiyan kasar bayan an kammala zaben shugaban kasa da ya kawo karshen rikicin siyasa a Madagascar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.