Isa ga babban shafi
Madagascar

Masu sa ido sun yaba da zaben Madagascar

Masu sa ido na kasashen Turai da Nahiyar Afrika da suka kalli yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa a Madagascar, sun yaba da yadda zaben ya gudana, wanda ake saran kammala tattara sakamakonsa cikin mako guda. Shugaban masu sa ido na Turai, Maria Muniz de Urquiza, tace zaben ya kai mizanin duniya kamar yadda ake bukata, ba tare da samun wata matsala ba.

Kuri'un zaben shugaban kasar Madagascar
Kuri'un zaben shugaban kasar Madagascar REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Yanzu haka ‘Yan takarar da ke samun goyan bayan shugaba Andry Rajoelina da hambararren shugaban kasa, Marc Ravolomanana ne ke kan gaba a zaben duk da an haramtawa shugabannin tsayawa takara a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.