Isa ga babban shafi
Madagascar

Ana ci gaba da jiran sakamakon zaben kasar Madagascar.

Jami’an hukumar zaben kasar Madagascar na ci gaba da lissafa sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar a jiya juma’a, tare da ‘yan takara fiye da 30 da suka shiga a cikin zaben.

Jami'an zabe a kasar Madagascar.
Jami'an zabe a kasar Madagascar. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Yanzu haka dai hukumar na ci gaba da wallafa sakamakon zaben a shafinta na yanar gizo, wanda hakan ke bai ‘yan takarar da magoya bayansu damar sanin halin da ake ciki, to sai dai daya daga cikin ‘yan takarar mai suna Robinson Jean-Louis, da ke samun goyon bayan hambararren shugaban kasar Marc Ravalomanana, ya ce bai debe tsammanin yin nasara a zaben tun a zagayen farko ba.

Al’ummar kasar dai sun Kagu jiran sakamakon zaben, da aka gudanar jiya.

Madagascar dai kasa ce dake a kan Tsibirin Indiya, kuma ta kasance ne cikin rikicin Siyasa Shekaru Hudu da suka gabata, tun bayan da Rajoelina ya hambarar da gwamnatin Marc Rovalomanana.

A halin da ake ciki kuma, an bayyana cewar tsohon Ministan Kudi na gwamnatin Adry Rajoelina wato Hery Rajaonarimampianina ne matsayin na biyu a Kuri’u da yawan Kuri’un da ya kai kashi 15.33%

Jami’an zaben dai nada kwarin Guiwar cewar tattara sakamakon zabe cikin hanzari nan gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.