Isa ga babban shafi
Madagascar

Ana zaben shugaban kasa a Madagascar

Al’ummar kasar Madagascar sun fara jefa kuri’ar zaben shugaban kasa, a karon farko cikin shekaru biyar, zaben da aka hana shugaba Andry Rajoelina da hambararen shugaban kasa, Marc Ravolomanana tsayawa takara domin samun zaman lafiya da dorewar Demokuradiya a kasar bayan juyin mulkin 2009.

Zaben Shugaban kasa a Madagascar
Zaben Shugaban kasa a Madagascar AFP PHOTO / STEPHANE DE SAKUTIN
Talla

‘Yan takara 33 ne ke neman lashe kujerar shugaban kasa, kuma masu lura da siyasar kasar sun ce babu wanda za’a iya cewa zai lashe zaben a zagaye na farko, Akwai yiyuwar sai an shiga zagaye na biyu.

Zaben wanda za’a gudanar, mataki ne na samun sauyin gwamnati kamar yadda masu shiga tsakanin rikicin kasar suka tsara bayan juyin Mulkin shekarar 2009.

Kasar Madagascar ta fada cikin rudanin siyasa da tabarbarewar tattalin arziki ne bayan da Rajoelina ya kwace Mulki.

A wani Rahoton Bankin Duniya, rahoton yace an samu karuwar talauci da kashi 92 bayan masu saka jari sun kauracewa kasar.

A shekarar 1960 ne kasar Madagascar ta samu ‘Yancin kai daga Turawan mulkin Mallaka na Faransa, kuma tun a lokacin kasar ta fada rikice rikice da dama.

Da Misalin karfe 6 na safe ne aka bude runfunan zabe inda mutanen kasar sama da Miliyan 7 ke da damar kada kuri’a.

Akwai masu sa ido da dama da suka hada da na kasashen waje wadanda za su lura da yadda zaben zai gudana duk da ana fargabar akwai matsala daga hukumar zabe game da samar da kayan aiki a cikin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.