Isa ga babban shafi
Najeriya

Jihohi suna neman karin kudi daga asusun Tarayya

Jihohin Najeriya sun bukaci gwamnatin Tarayyar ta kara masu kudaden da yawansu ya kai dala bilyan biyu domin cike gibin da suke fuskanta sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya.

Ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala.
Ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Wani kwamitin kwamishinonin kudi na jihohin kasar 36 suka kafa, shi ne ya nemi bukatar daga gwamnatin Tarayyar, inda kwamitin ya ce matukar aka wuce tsakiyar watan disambar bana ba tare da an yi masu wannan kari ba, za a wayi gari wasu daga cikin jihohin su kasa biyan albashin ma’aikatansu da kuma dakatar da wasu ayyuka na ci gaban al’umma.

Shugaban kungiyar kwamishinonin kudi Mista Timothy Oddah, na jihohin kasar, ya ce hatta kudaden da ake kira da sunan asusun tsaro da ake da su a gwamnatocin jihohi, na daga cikin wadanda ke fuskantar wannan barazan kafin zabukan da ake shirin gudanarwa a kasar a cikin watan fabarairun shekara mai zuwa.

A karshen makon da ya gabata ne dai ministar ma’aikatar kudin kasar ta bayyana cewa dole sai gwamnatin ta tsuke bakin aljihunta sakamakon faduwar farashin mai a kasuwar duniya, lamarin da zai shafi yawan kudaden da jihohi ke samu daga asusun na Tarayya.

Yanzu haka hankula sun karkata zuwa ga taron koli na kungiyar kasashen da ke da arzikin mai wato OPEC da ake shirin gudanarwa a cikin makon gobe.

Sai dai hasashe na nuni cewa kasuwar ta mai za ta yunkuro domin dawo da kimarta bayan kammala taron, amma da sharadin cewa kasashen da ke fitar da mai, su rage adadin wanda suke fitarwa a rana.

Hukumar makamashi ta kasar Amurka DOE, na daga cikin wadanda ke hasashen cewa darajar man za ta farfado a cikin gajeren lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.