Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya sun karbe Chibok

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kwace garin Chibok daga hannun kungiyar Boko Haram kwanaki biyu bayan kama garin inda Mayakan suka sace ‘Yan matan Makaranta sama da 200 a watan Afrilu.

Yankin Chibok inda Mayakan Boko Haram suka sace 'Yan Mata sama da 200.
Yankin Chibok inda Mayakan Boko Haram suka sace 'Yan Mata sama da 200. news.softpedia
Talla

Mai Magana da yawun rundunar Kanal Sani Usman ya ce Chibok tana hannun Sojin Najeriya, kamar yadda ya tabbatar wa RFI Hausa.

01:03

Kanal Sani Usman

Bashir Ibrahim Idris

Kanal Usman yace tun a ranar Assabar ne Sojoji suka kwace garin Chibok tare da korar Mayakan Boko Haram daga garin.

Amma mazauna Chibok sun ce Sojojin sun kwace garin ne tare da taimakon ‘yan kato da gora.

Najeriya dai na ci gaba da fama da tabarbarewar tsaro, musamman a arewacin kasar.

A ranar Lahadi wata mace ta kai harin kunar bakin wake a garin Azare a Jihar Bauchi inda aka samu mutuwarmutane akalla 13.

A ranar alhamis ne boko Haram ta kwace garin Chibok bayan musayar wuta da Sojoji.

00:57

Shedun gani da ido a Harin Azare

Bashir Ibrahim Idris

Boko Haram ta kwace garuruwa kusan guda 20 a Jihohin da ke arewa maso gabacin Najeriya.

Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi na biyu ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su kare kansu daga barazanar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.