Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta fara zartar da Shari’a

Mayakan Boko Haram na Najeriya sun aiko da wani sabon sakon bidiyo da ke nuna Shugaban kungiyar Abubakar Shekau yana yi wa Jama’a wa’azi a wani gari da suka kwace a yankin arewa maso gabacin kasar.

Aboubakar Shekau Shugaban Mayakan Boko Haram a Najeriya
Aboubakar Shekau Shugaban Mayakan Boko Haram a Najeriya AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Hoton Bidiyon ya nuna shugaban Kungiyar yana yi wa mutane wa’azi tare da furuta nuna goyon bayansa ga Mayakan IS da suka mamaye wasu yankuna a Iraqi da Syria.

Mayakan dai sun aiko da bidiyon ne domin tabbatar wa duniya cewa sun kafa sabuwar daula.

A cikin bidiyon shekau ya nanata yin watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Najeriya ke ikirarin ta cim ma da su, tare da barazanar kisan mutumin da ke tattaunawa da gwamnati a madadinsu.

Rahotanni da ke fitowa daga garuruwan da Boko Haram ta kwace na cewa, mayakan sun fara zartar da hukunci na yanke hannu ga wadanda suka yi sata tare da kona wuraren ibadar mabiya addnin Kirista.

Kuma wasu rahotannin sun ce boko Haram ta sauya sunan garin Mubi da suka kwace a Jihar Adamawa zuwa Madinatul Islam. Haka kuma sun sauya sunan garin Gwoza da suka kwace a Borno zuwa Darul Hikma

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.