Isa ga babban shafi
Libya

An zabi sabon shugaban Majalisar Dokoki a Libya

A daidai lokacin da ake ci gaba da fama da yakin basasa, sabuwar Majalisar Dokokin kasar Libya ta zabi sabon shugaba a wani zama da ta gudanar a garin Tobrouk da ke gabashin kasar sakamakon yadda birnin Tripoli ya gagari ‘yan siyasa shiga.

'Yan bindiga a Libya
'Yan bindiga a Libya
Talla

To sai dai ‘yan majalisar da suka fito daga jam’aiyyar masu kishin Islama, sun kaurace wa zaman da kuma zaben da aka yi a a ranar litinin, inda suka bukaci a gudanar da zaman a Tripoli cikin ginin Majalisar.

Yanzu haka dai ana ci gaba da gwabza fada ne tsakanin ‘yan tawayen da suka fito daga garin Zintane da kuma Misrata ke fafatawa da juna domin kama birnin Tripoli.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.