An kai wa Sarakunan Borno hari
Rahotanni daga Najeriya na cewa Mayakan Boko Haram sun kai wa wasu Sarakunan Gwoza da Uba da Askira hari a Masarautar Borno a lokacin da suke kan hanyarsu zuwa ta'aziyar rasuwar Sarkin Gombe, Wasu rahotannin sun ce 'Yan bindigar sun kashe Sarkin Gwoza Shehu Idris Timta.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A safiyar Juma’a ne ‘Yan bindigar suka kai wa Sarakunan hari a kan hanyarsu zuwa garin Gombe domin ta’aziyar rasuwar Sarkin Gombe wanda ya rasu a Asibitin London a ranar Talata.
Wata majiya da ke kusa da masarautar Borno ta tabbatar da faruwan al’amarin.
Sanata Ali Ndume Dan Majalisa da ke wakiltar yankin Gwoza a Jahar Borno yace ya tattauna da Sarakunan Askira da Uba amma bai samu ya zanta da Sarkin Gwoza ba da aka ruwaito ‘Yan bindigan sun kashe shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu