Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Wani Sojan Najeriya ya zargi Shugabanninsu

Wani Jami’in rundunar sojan Najeriya wanda yanzu haka ya ke yankin arewa maso gabaci da ke fuskantar hare haren Boko Haram yace rashin kayan aiki na daga cikin dalilan da ke haifar da tarnaki ga ayyukansu a zantawarsa da Sashen Hausa na Rediyo Faransa.

Kakakin rundunar Sojin Najeriya Chris Olukolade
Kakakin rundunar Sojin Najeriya Chris Olukolade REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A Najeriya, an jima ana zargin sojojin kasar da nuna gazawa wajen tunkarar Mayakan kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da addabar arewacin kasar.

Sojan wanda ya nemi a sakaye sunansa yace sun san inda mayakan Boko Haram suke buya amma akwai manyansu da ba su son a kawo karshensu.

“Muna bukatar Makamai don mu yaki Boko Haram” a cewar Sojan.

Ya kuma ce Mayakan Boko Haram sun mallaki muggan makamai da suke kisan Jama’a.

Akwai dokar ta-baci da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kafa a Jahohin Borno da Yobe da Adamawa domin yaki da mayakan Boko Haram.

03:10

Tattaunawa da Sojan Najeriya

Abdoulkarim Ibrahim

Amma tun kafa dokar kashe kashen da aka samu sun zarce wadanda aka samu kafin kafa dokar.

A cikin hirarsa da Rediyo Faransa, Sojan na Najeriya yace su kansu ba su yarda da kansu ba domin mutum ba ya iya tantance Soja da Mayakan Boko Haram da ke kai hare hare sanye da Kakin Soja.

Wannan kuma ke sa alamar tambaya akan ko yaushe za’a kawo karshen rikicin Boko Haram a Najeriya?

A cikin jawabinsa ga ‘Yan Najeriya a ranar bikin dimokuradiya, shugaba Goodluck Jonathan yace a shirye ya ke ya yi yaki ta’addanci a kasar domin kare mulkin demokuradiya, amma an kwashe shekaru biyar kasar na fama da matsalar tsaro, inda yanzu sace ‘Yan mata sama da 200 a garin Chibok ya ja hankalin duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.