Jonathan zai yi yaki da ta’addanci don kare dimokuradiya
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sha alwasin yaki da ta’addanci domin kare demokuradiya da aka kwashe shekaru goma sha biyar kasar na cin moriya. Shugaban ya fadi haka ne a cikin jawabinsa ga ‘Yan kasa a ranar bikin dimokuradiya.
Wallafawa ranar:
Shugaban yace hadin kan kasa da dorewar mulkin demokuradiya na fuskanta barazana daga hare haren ta’addanci.
Shekaru 15 ke nan da Najeriya ta dawo mulkin demokuradiya daga mulkin Soji, amma yanzu an kwashe shekaru sama da biyar kasar na fama da tabarbarewar tsaro inda dubban mutane suka mutu.
Batun sace ‘Yan matan Chibok sama da 200 kuma ya ja hankalin duniya, inda yanzu manyan kasashen irin su Amurka da Faransa da Birtaniya suka aiko da kwararru domin kokarin kubutar da ‘Yan matan da mayakan Boko Haram suka sace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu