Isa ga babban shafi
MDD-Najeriya

Boko Haram ta shiga cikin kungiyoyin ta’addanci a duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta jefa kungiyar Boko Haram cikin jerin kungiyoyin ‘Yan ta’adda kuma wacce aka bayyana tana da alaka da Kungiyar Al Qaeda tare da sanya wa kungiyar Takunkumi.

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau As received by Reuters
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Nigeria ke ci gaba da zanga zangar neman kungiyar Boko Haram ta sako wasu ‘yan mata fiye da 200, da ta yi awon gaba da su a wata makarantar Sakandare a garin Chibok da ke Jihar Borno.

Tuni Amurka ta yi na’am da matakin musamman takunkumin da aka saka wa Kungiyar da ya shafi rufe asusu da cininkin makamai, kodayake ba a san tasirin da matakin zai yi ba.

Kwamitin takunkumi na Majalisar Dinkin Duniya yace zai yi kokarin daukar matakai wajen dakile tallafin da Kungiyar ke samu.

Kwamitin yace akwai hujjoji da ke nuna kungiyar Boko Haram ta samu horo daga Mayakan al Qaeda a reshen Maghreb wadanda suka yi aiki tare da arewacin Mali.

Dubban mutane ne suka mutu sakamakon hare haren Kungiyar Boko Haram a Najeriya. Masana suna ganin babu wani tasiri da takunkumi zai yi akan Kungiyar da har yanzu ba a san bukatunsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.