Isa ga babban shafi
Faransa-Najeriya

Faransa da Makwabtan Najeriya za su yi yaki da Boko Haram

Shugaba Francois Hollande na Faransa, da takwarorinsa na Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Benin, sun amince da yin aiki a tare domin murkushe Mayaka Boko Haram da suka addabi arewacin Najeriya. Shugabannin sun ce ayyukan Kungiyar babbar barazana ce ba wai ga Najeriya kawai ba har ma da sauran kasashe.

Francois Hollande, shugaban Faransa tare da Shugabannin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Jamhuriyyar Benin a Paris
Francois Hollande, shugaban Faransa tare da Shugabannin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Jamhuriyyar Benin a Paris Présidence de la République
Talla

Shugabannin sun bayyana haka ne a wani taro da suka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa.

Shugaban kasar Faransa mai masaukin baki a wanna taron Francois Hollande, ya bayyana cewa ta la’akari da salon fadan kungiyar Boko Haram, dole ne a dauki matakai domin kawo karshen ayyukanta cikin gaggawa.

Hollande yace Kungiyar tana dauke da manyan makamai irin na zamani, sannan kuma take da cikakken horo kan yadda ake sarrafasu.

A cewarsa magoya bayan kungiyar sun samu horo a lokacin da yankin arewacin Mali ke karkashin mamayar ‘yan ta’adda, kuma bisa ga dukkan alamu kungiyar tana da makudden kudade.

Shugaban kasar Chadi, Idris Deby, yace bai kamata a zura wa Mayakan Boko Haram ido suna ci gaba da kashe jama’a ba.

“Kungiya ce da ta tuni ta yi mummunan ta’addi, ci gaba da wanzuwarta, na nufin bai wa ta’addanci gidin zaman”, a cewar Shugaban Chadi.

Kuma Shugaban yace yanzu sun tsara daukar matakai da dama, a gaggauce da kuma lokuta masu zuwa.

Kasar Kamaru da ake cewa Mayakan Boko Haram sun kutsa kai a cikin kasar, shugaba Paul Biya, yace Boko Haram ta fice daga matsayin kungiyar da ke haifar da matsala ga Najeriya domin yanzu a cewarsa ta zama karfen kafa ga kasashen yankin da kuma Afrika baki daya.

Faransa ta kira taron ne bayan Mayakan na Boko Haram sun sace ‘Yan mata sama da 200 daliban Makaranta Sakandare a garin Chibok a cikin Jahar Borno.

Yanzu dai an zura ido domin ganin matakan farko da kasashen za su dauka na dakatar da hare-haren kungiyar kafin murkushe ayyukanta baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.