Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane Biyar sun Mutu a harin Kano

Akalla mutane biyar suka mutu cikinsu har da wata karamar Yarinya a wani harin kunar bakin wake da aka kai a Birnin Kano a arewacin Najeriya, kamar yadda rundunar ‘Yan sandan Jahar ta tabbatar.

Wasu hare haren Bama bamai da Mayakan Boko Haram suka kai a Jahar Kano a Najeriya
Wasu hare haren Bama bamai da Mayakan Boko Haram suka kai a Jahar Kano a Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Magaji Musa yace a wajajen misalin karfe 10 na dare ne aka kai harin Kunar bakin wake a Unguwar Sabon Gari kuma cikin wadanda suka mutu har da maharin da ya kai harin a cikin mota.

Harin kuma na zuwa ne bayan kammala zaben Kananan hukumomi inda Jam’iyyar Adawa ta APC mai adawa da PDP ta shugaba Goodluck Jonathan ta lashe kujerun shugabannin Kananan Hukumomin 44.

01:29

Rahoton Abubakar Isa Dandago daga Kano

Abubakar Issa Dandago

A bara an taba kai hare haren bama bamai a Unguwar Sabon Gari a Kano inda mutane akalla 12 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.