Isa ga babban shafi
Nigeria

Arangama tsakanin jami'an tsaro da mazauna birnin Maiduguri

Rahotanni daga birnin Maiduguri na tarayyar Najeriya na cewa direbobin Keke-Napep da kuma sauran al’ummar garin sun gudanar da wata mummunar tarzoma, bayan da wani jami’in tsaro ya harbe direban wannan mashin da ake amfani da shi wajen gudanar da sana’ar Acaba da kuma wani fasinja daya.

Zagayen kasuwar Maiduguri Najeriya
Zagayen kasuwar Maiduguri Najeriya RFI/Nicolas Champeaux
Talla

Lamarin dai ya faru ne da misali karfe 11 na safiyar yau a wata unguwa mai suna West End da ke birnin, kuma bayan da labari ya bazu a cikin gari, sai daruruwan jama’a, suka fantsama kan tituna, yayin da wasu suka tunkarar ofishin ‘yan sanda na Dandal Police Station domin nuna fushinsu.

Har ila yau rahotanni sun ce an yi kone-kone a wasu unguwanni, yayin da kuma ake kyautata zaton cewa an samu asarar rayuka sakamakon yadda jami’an tsaro suka rika harbi domin kange masu zanga-zangar da suka nufin cibiyoyin ‘yan sanda da ke birnin.

A daya bangare kuwa rahotanni na cewa an yi dauki ba-dadi tsakanin jami’an tsaro da kuma wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton cewa magoya bayan kungiyar Boko haram ne a birnin na Maiduguri a yau lahadi.

Shaidu sun ce an yi artabun ne a unguwar Gwange da ke birnin, bayan da aka samu fashewar wasu abubuwa. Kawo yanzu dai babu karin bayani a game da asarar da aka sama a wannan sabon fada ba.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.