Boko Haram barazana ce ga Yammaci da Tsakiyar Afirka
Shugaba Francois Hollande na kasar Faransa, ya ce dole ne kasashen duniya su hada gwiwa domin kawo karshen ayyukan Boko Haram, kungiyar da ya ce a yau ta zama babbar barazana ga tsaro ga Najeriya da sauran kasashen Yammaci da kuma Tsakiyar Afirka.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hollande, wanda ke gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru, Chadi da kuma Benin da ke halartar taro kan wannan batu a birnin Paris, ya ce ko shakka babu akwai alaka tsakani Boko Haram da kuma kungiyar Aqmi wato reshen Alqa’ida a arewacin Afirka.
Francois Hollande ya ce Faransa ba ta da niyyar tura sojojinta zuwa Najeriya a halin yanzu, amma kuma za ta yi aiki da sauran kasashen duniya domin murkushe ayyukan wannan kungiya.
Taron dai na samun halartar shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, da takwaransa Issifou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar, da shugaban Chadi Idris Deby Itno, da Bony Yayi na jamhuriyar Benin da kuma Paul Biya na Kamaru.
Har ila yau akwai wakilai daga Birtaniya da kuma Kungiyar tarayyar Turai da ke halartar wannan taro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu