Isa ga babban shafi
Najeriya-Turai

Amurka ta fara laluben Malabar Boko Haram

Kasar Amurka ta fara aikin lalaben Malabar ‘ya’yan kungiyar Boko Haram masu garkuwa day an Mata fiye da 200 da suka sace daga wata Makaranta a Chibok ta jihar Borno

Talla

Yanzu haka dai Jiragen yakin kasar Amurka na ci gaba da sintiri ta sararin samaniya a ani aiki na ci gaba da lalaben ‘yan matan nan da kungiyar Boko Haram ta bayyana yin garuwa da su akalla Wata daya da ya gabata.

Wannan dai na zuwa ne bayan da fadar shugaban kasar ta Abuja ta yi watsi da tayin musayar fursunonin Boko Haram da gwamnatin Goodluck Jonathan ke tsare da su da kungiyar Boko Haram din ke bukatar a saka kamin su saki ‘yan matan.

Wani babban jami’in hukumar leken Asiri na Amurka ya fada a Najeriya cewar yanzu haka Amurka na amfani da Tauraron dan Adam masu sunsuno taswrar ban kasa domin dauko hoton Malabar kungyar ta Boko Haram.

Sai dai ba’a amince a sanar da sunan babban jami’in hukumar ta Amurka ba, kuma babu bayani akan samfurin Jiragen da Amurka ke amfani da su a wannan aikin a Najeriya ba.

Haka ma ba’a fayyacewa Duniya bagiren da Dakarun Amurkar ke fakewa ba, domin kiyaye sirri.

A baya-bayan nan dai ne shugaban kungiyar Boko haram a Najeriya Abubakar Shekau ya bayyana daukar alhakin sace ‘yan matan na garin Chibok da ke a Hannun su yau sama da Wata daya kenan.

A cikin wani Hoton Bidiyo na mintoci 27 Abubakar Shekau ya nuna akalla mata 130 da ya ce sun sauya sheka kuma sanye da Hijabbai.

Akalla dai Mata 276 ne ‘ya’yan kungiyar ta Boko Haram suka kama inda Alkalumman Gwamnati ke nuna cewar har yanzu akwai akalla Mata 223 da ba’a da tabbas akan makomarsu.

Ana dai ci gaba da sukar Najeriya akan yanda take saku-saku da batun kwato ‘yan matan, amma kuma ta fuskanci kalubale ainun daga Gwamnatocin kasa-da-kasa.

Shugaba Goodluck Jonathan dai ya karba tayin kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da China da Israela ne, domin gano inda ‘ya’yan boko Haram ke rike da Matan, da kuma tuni suka aike da kwararru domin soma wannan aikin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.