Isa ga babban shafi
Najeriya-Faransa

Chibok: Faransa ta kira taron Afrika a Paris

Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande, ya bukaci shugabanin kasashen Afrika ta Yamma su halarci wani taro a birnin Paris wanda zai mayar da hankali kan sace dalibai mata sama da 200 da aka yi a garin Chibok a Najeriya.

Mata masu zanga-zangar neman a sako 'yan matan Chibok
Mata masu zanga-zangar neman a sako 'yan matan Chibok REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Shugaba Hollande ya bayyana haka ne a kasar Azerbaijan, bayan ya tattauna da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan game da taron wanda za’a yi a ranar Assabar mai zuwa, tare da shugabannin kasashen Chadi da Kamaru da Nijar da Jamhuriyar Benin.

Yanzu haka kasar Isra’ila ta shiga sahun kasashen duniya da suka yi tayin taimakawa Najeriya gano ‘Yan mata daliban Makaranta 223 da Mayakan Boko Haram suka sace tsawon wata guda.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya amince da tayin na Isra’ila bayan ya tattauna da Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ta wayar Tarho, kamar yadda kakakinsa Reuben Abati ya tabbatar.

Tuni Birtaniya da Amurka da Faransa suka aika da tawagar kwararru zuwa Najeriya domin taimakawa dakarun kasar kubutar da ‘Yan matan da aka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.