Isa ga babban shafi
Najeriya-Amnesty

Kungiyar Amnesty International ta soki hukumomin Najeriya

Kungiyar kare hakin Bil’adama ta Amnesty International a rahoton da ta fitar yau juma’a, ta ce an aikewa da sojojin Nijeriya da wani gargadi mai cewa akwai yiyuwar kungiyar Boko Haram na shirin yin garkuwa da ‘yan makarantar nan da aka kwashe a garin Chibok na  jihar Borno.  

wasu mutanen garin Chibok dake  Jihar Borno.
wasu mutanen garin Chibok dake Jihar Borno. Reuters/Stringer
Talla

kungiyar Amnesty ta ce duk da wannan gargadi jami’an gwanatin kasar ba su dauki matakan hana faruwar lamarin ba har sai da ‘yan Boko Haram suka kai hari tare da kwashe ‘yan matan.

A cewar rahoton sojojin ba su iya dakile wannan barazanar ta kungiyar ba sakamakon rashin kayan aiki da kuma tsoron arangama da yan kungiyar da ke da kayan yaki na zamani.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.