Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya yi watsi da sharadin Boko Haram

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yace babu batun musayar fursunonin Mayakan kungiyar Boko Haram da ‘Yan mata daliban Makaranta da mayakan suka sace a garin Chibok kamar yadda Kwamandan Boko Haram Abubakar Shekau ya bukata.

Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya
Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya Reuters/Eduardo Munoz
Talla

Jonathan ya bayyana haka ne, yayin da ya ke ganawa da Ministan Afrika na kasar Birtaniya Mark Simmonds wanda ya kai ziyara a Abuja.

Mista Simmonds yace Shugaban Najeriya ya jaddada masa cewa babu batun tattaunawa da Boko Haram akan musayar fursononi.

A cikin sakon bidiyon da Kungiyar Boko Haram ta aiko, Abubakar Shekau yace ba zai saki ‘Yan matan ba da ya nuna hotonsu sanye da Hijabi suna karatun Qur’ani har sai mahukuntan Najeriya sun saki Mayakan shi.

Akwai Ministan ayyuka na musamman Tanimu Turaki da ya bude kofar tattaunawa da Boko Haram domin kubutar da ‘Yan matan, amma kuma yanzu jekadan Birtaniya yace Shugaba Jonathan ya yi watsi da matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.