Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta yi tayin sulhu da Boko Haram

Bayan shafe tsawon wata guda da sace ‘Yan mata daliban Makaranta sama da 200 a Chibok da ke cikin Jahar Borno a yankin arewacin Najeriya, Gwamnatin kasar tace a shirye ta ke ta hau teburin sulhu da Mayakan Boko Haram da suka sace ‘Yan matan.

'Yan Matan da Kungiyar Boko Haram ta sace a Chibok sanye da Hijabi
'Yan Matan da Kungiyar Boko Haram ta sace a Chibok sanye da Hijabi AFP
Talla

Ministan ayyuka na Musamman Tanimu Turaki ne ya yi wannan tayin wanda da dadewa ke jagorantar kwamitin da gwamnatin Jonathan ta kafa na yunkurin tattaunawa da Boko Haram.

“Mu a shirye mu ke mu hau teburin sulhu da Boko Haram akan duk batutuwan da ke kan tebur har da batun ‘Yan mata da aka sace” a cewar Kabiru Turaki.

Sai dai kuma Ministan yace lura da abin da ya faru a baya suna shakku da sharadin na Boko Haram domin kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba a baya bayan kwamitin sulhu ya bukaci Jami’an tsaro su saki mambobin Kungiyar da suka hada da Matar Shekau da kanwarsa.

“idan ma Gwamnati tace zata yadda akai ga matsayin ba ni gishiri in ba ka manda to da wa za’a zauna” Inji Turaki yana mai bayyana shakku akan Boko Haram.

Tuni dai Ministan cikin gida ya yi watsi da sharadin shugaban Boko Haram Abubakar Shekau akan zai saki ‘Yan matan idan an saki mayakan shi da ke hannun Jami’an tsaro.

Kungiyar Boko Haram ta dade tana kai hare hare a arewacin Najeriya, amma batun sace ‘Yan mata shi ya ja hankalin duniya wadanda galibinsu Kiristoci ne. Kuma Kungiyar Boko Haram ta aiko da hoton bidiyon ‘Yan matan suna sanye da Hijabi a matsayin sun karbi Musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.