An rufe wata jarida a Jamhuriyar Nijar
Hukumomi a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, sun bayar da umurnin rufe wata jarida mai suna Le Courrier, wadda ta shahra wajen sukar lamarin gwmanatin shugaba Issifou Mahamadou.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mawallafin jaridar Ali Soumana, ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan sanda ne suka rufe ofishin jaridar, to sai dai Ali Soumana ya ce ba wani dalilin da ‘yan sanda suka gabatar dangane da daukar wannan mataki.
Har ila yau ko baya ga jaridar ta Le Courrier, ‘yan sanda sun rufe ofisoshin wasu kungiyoyin kwadago biyu a birnin na Yamai, cikinsu har da kungiyar direbobin motocin Taxi da ta shahra wajen gudanar da yajin aikin neman a rage farashin man fetur a kasar wato kungiyar da ake kira Syncotaxi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu