Isa ga babban shafi
Najeriya

An sako ‘yan mata dalibai goma cikin wadanda aka sace a Jihar Borno

Rahotanni da dimi-dimi daga jihar Borno Nigeria na cewa ‘yan bindiga da suka sace ‘yan mata masu tarin yawa tun a ranar litinin din da ta gabata sun sako 10 daga cikinsu a  yau Laraba.

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Talla

Kwamishinan Ilmi na jihar Musa Inuwa Kubo ya gaskata cewa an sako ‘yan matan ba tare da ko kwarzane a jikinsu ba.

A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari wata makarantar kwana ta mata a garin Chibok dake jihar ta Borno inda suka yi awun gaba da dalibai sama da hamsin dukkaninsu mata.

Wannan lamari ya auku ne kwanaki kadan bayan da wasu mahara suka hari a yankin inda suka kashe sama da mutane 70.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.