Isa ga babban shafi
Najeriya-Turai

Kungiyar Turai ta damu da hare haren ta’addanci a Najeriya

Babbar Jami’ar kula da harakokin wajen Kungiyar kasashen Turai Catherine Ashton ta yi tir da dalibai mata da ‘Yan bindiga suka sace a Chibok cikin Jahar Borno a arewacin Najeriya, tare da bayyana damuwa akan ayyukan ta’addanci da ke faruwa a Najeriya.

Wasu mata suna kuka a kusa da asibitinin Asokoro bayan sun ga yadda ake shigar da gawarwakin mutane da suka mutu a harin Nyanya da aka kai da safiyar Litinin.
Wasu mata suna kuka a kusa da asibitinin Asokoro bayan sun ga yadda ake shigar da gawarwakin mutane da suka mutu a harin Nyanya da aka kai da safiyar Litinin. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A cikin wata sanarwa, Ashton ta yi Allah wadai da sace dalibai sama da 100 a Chibok, kwana guda bayan wani munmunan harin bom da aka kai a Nyanya a Abuja wanda ya hallaka rayukan mutane sama da 70.

Ashton tace kungiyar Turai tana bayan mutanen Najeriya da gwamnatin kasar wajen yaki da ta’addanci da kare hakkin mutane.

A ranar Litinin ne ‘Yan bindiga suka abka cikin wata Makarantar sakandare suka sace dalibai mata a Chibok a Jahar Borno, a lokacin da kuma al’ummar Najeriya ke juyayin harin bom da aka kai a tashar shiga mota a Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.