Cote d'Ivoire
Cote d’Ivoire ta mika Ble Goude zuwa Hague
Kasar Cote d’Ivoire ta ce ta mika Charles Ble Goude na hannun damar tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo zuwa kotun hukunta laifukan yaki ta ICC a Hague.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Tun a watan Oktoba ne Kotun ICC ta bayar da sammacin cafko Ble Gaoude wanda ya jagoranci mayakan sa-kai a zaben shugaban kasa da Gbagbo ya ki mika mulki bayan sha kaye.
A cikin wata sanarwa kotun ICC tace zata yi aiki da gwamnatin Cote d’Ivoire domin ganin yadda za’a mika Ble Goude zuwa Hague.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu