Ble Goude ya nemi kada a mika shi zuwa ICC
Shugaban Kungiyar ‘Yan ina da kisa Charles Ble Goude a karkashin tsohuwar gwamnatin kasar Cote d’Ivoire, ya bukaci gwamnatin kasar da kar ta mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka don fuskantar shari’ar kisan kai da fyade, yana me bukatar a yi masa shari’a a gida. Lauyan wanda ake zargin, Claver N’Dri, yace sun mika bukatarsu ga gwamnatin kasar, na ganin an yi wa Ble Goude shari’a a gida, saboda imanin da suke da shi cewar kotunan kasar za su iya yin adalci.
Wallafawa ranar:
Ble Goude wanda shi ne na hannun damar Gbagbo ana zarginsa ne da mallakar wata kungiya da ta kashe mutane kusan 3,000 da ke adawa da shugaban kasa na yanzu Alassane Ouattara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu