Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Amnesty ta zargi Dakarun Cote d’Ivoire da laifin keta hakkin Bil’adama

Kungiyar kare hakkin Bil adama ta Amnesty International ta zargi sojojin kasar Cote d’Ivoire da aikata laifukan take hakkin magoya bayan tsohon Shugaba Laurent Gbagbo a rikicin siyasar kasar day a biyo bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Nuwamban 2010.

'Yan sandan Cote d'Ivoire suna arangama da magoya bayan tsohon shugaba laurent Gbagbo a Abidjan
'Yan sandan Cote d'Ivoire suna arangama da magoya bayan tsohon shugaba laurent Gbagbo a Abidjan AFP PHOTO/ SIA KAMBOU
Talla

A wata ziyara da Kungiyar Amnesty International ta kai kasar Cote d’Ivoire a watannin Satumba da Oktoban da suka gabata, kungiyar ta gano an muzgunawa magoya bayan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, inda rahotan ya bayyana cewa ana kisan kai da kuma tsare mutane ba tare sun ji sun gani ba.

A cewar rahotan, sojojin suna yin hakan ne da fakewar suna so su dakile ayyukan hare hare da ake kai wa a kasar, inda kungiyar ta ce ta tattara bayananta ne bayan sauraren wasu da abin ya shafa, wadanda wasunsu aka azabtar da yin amfani da wutar lantarki.

Kungiyar ta kara da cewa, wasu iyalan ba su san inda ‘yan uwansu su ke ba sai bayan kungiyar ta fitar da bayanai, wadanda iyalan suka yi amfani da su suka gano inda ‘yan uwan na su suke.

Sabuwar rundunar sojin kasar ta Cote d’Ivoire an hade ta ne bayan hankula sun kwanta daga rikicin da ya biyo bayan zaben kasar inda akalla mutane sama da 3,000 suka rasa rayukansu bayan Gbagbo ya ki mika mulki ga Alassane Ouattara wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.