Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Al’ummar Cote d’Ivoire suna bukin samun ‘Yancin kai cikin dar-dar

A yau Talata ne kasar Cote d’Ivoire ke bukin cika shekaru 52 da samun ‘Yancin kai daga Turawan Faransa, sai dai bukin na zuwa ne bayan kai wani hari a sansanin Soji a birnin Abidjan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane Shida.

Dakarun Cote d'Ivoire da ke sintiri a birnin Abidjan
Dakarun Cote d'Ivoire da ke sintiri a birnin Abidjan REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Shuagaba Alassane Ouattara yace an karfafa matakan tsaro a sassan yankunan kasar a kokarin magance yaduwar Makamai bayan kawo karshen rikicin siyasar Kasar.

A ranar Litinin ne wasu ‘Yan Bindiga suka bude wuta a kusa da Sansanin Sojin Akuuedo da ke birnin Abidjan. Mazauna garin sun ce ‘Yan bindigar sun fara kai harin ne a sansanin Soji kafin su abka wa ginin mujallar Powder.

Rahotanni sun ce wadanda suka mutu dukkaninsu Sojoji ne kuma wasunsu da dama suka samu rauni.

Wata Majiya daga gwamnatin kasar tace ‘Yan bindigar sun kai harin ne domin neman sakin mutanen da aka cafke kwanan baya.

Al’ummar kasar Cote d’Ivoire yanzu haka suna cikin fargaba da zaman dar dar duk da kawo karshen watanni Biyar na rikicin kasar da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a watan Disembar shekerar 2010 inda tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo ya ki amincewa ya mika mulki ga Ouattara bayan ya sha kaye a zabe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.