Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire-MDD

‘Yan gudun Hijirar a Cote d’Ivoire sun ce MDD ta gaza wajen kare su

‘Yan Gudun hijira da a ke kai wa hari a sansaninsu da ke Cote d’Ivoire, sun zargi dakarun Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen kare su. Bayan mutuwar mutuwar mutane bakwai da raunana wasu 50.

Sansanin 'Yan gudun Hijira a kasar Cote d'Ivoire
Sansanin 'Yan gudun Hijira a kasar Cote d'Ivoire Reuters
Talla

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya, da na gwamnatin Cote d’Ivoire, sun zargi junansu kan harin daukar fansa da wasu mutane 300 dauke da makamai suka kai, sakamakon fashin da aka yi wa wasu daga cikin su.

Daya daga cikin mutanen da harin ya ritsa da su, mai suna Sidikhi Dembele, yace lokacin da aka kai musu harin, ya ruga da gudu inda ya hau motar dakarun Majalisar Dinkin Duniya, amma sai suka ture shi kasa, abinda yasa maharan suka kama dukansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.