An yanke wa janar din Gbagbo hukuncin Dauri a Cote d’Ivoire
Kotun Cote d’Ivoire ta yanke wa Wani babban Kwamandan Soji kasar hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari, wanda ya yi zamani da tsohon shugaba Laurent Gbagbo. Wannan ne kuma hukunci na farko da kotun ta yanke jami’an Gwamnatin Gbagbo da suka taka rawa a rikicin siyasar kasar.
Wallafawa ranar:
Janar Bruno Dogbo Ble shi ne shugaban tsaro ta Republican Guard a lokacin rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 3,000 bayan Gbagbo ya ki amincewa ya mika mulki ga Alassane Ouattara a zaben da ya sha kashe da aka gudanar a shekarar 2010.
Kotun ta kama Mista Dgono Bled a laifin garkuwa da mutane da kuma tare da mutane ba bisa ka’ida ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu