Isa ga babban shafi
Nijar

Majalisa za ta duba makomar sojojin ketare a Jamhuriyar Nijar

Ayarin farko na sojojin kasashen ketare suka shiga kasar su ne sojan Faransa wadanda aka tura jim kadan bayan da wasu mahara suka sace Faransawa da ke aiki a kamfanin Areva da ke garin Arlit a ranar 16 ga watan satumbar shekarar 2011.

SHugaban Nijar Issifou Mahamadou tare da rakiyar sojojin kasar
SHugaban Nijar Issifou Mahamadou tare da rakiyar sojojin kasar RFI/Sonia Rolley
Talla

To sai dai a maimaikon birnin Arlit da ke arewacin kasar, an ci gaba da ganin Faransawan hatta ma a cikin birnin Yamai da kuma sauran yankunan kasar dauke da manyan makamai har ma da jiragen yaki, yayin da jama’a ke ci gaba da diga ayar tambaya dangane da dalilai kasantuwarsu a kasar.

Wanzuwar sojojin kasashe yamma kamar Faransa da kuma Amurka a jamhuriyar Nijar ba wani boyayyen abu ba ne, domin kuwa akan gan su a fili musamman a birnin Yamai da kuma wasu johohin kasar kamar Agadez da Diffa da kuma arewacin Tillaberi mai iyaka da kasar Mali.

Ita dai gwamnatin Nijar ta bayyana cewa dole ne a hada da kasashen ketare domin tunkarar matsalar ta’addanci da ta addabi yankin da kuma duniya baki, musamman ma ta la’akari da halin da ake cikin a kasashen Libya, Algeria, Mali da kuma Tarayyar Najeriya masu makotaka da kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.