Isa ga babban shafi
Niger-Libya

Nijar ta mika Saadi Ghaddafi zuwa Libya

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun mika dan tsohon shugaban kasar Libya Sa’adi Ghaddafi a hannun hukumomin Tripoli.

Talla

Sa’adi kaddafi, wanda ya gudu daga Libya a shekara ta 2011, ya samu mafaka a birnin Yamai, to amma a yau da safe, kafafen yada labaran Libya sun nuna hotunsa a hannun jami’an tsaron kasar.

Hukumomin kasar ta Libya sun ce za a rike Sa’adi a matsayin fursuna kamar yadda dokar kasa da kasa ta tsara kan fursunoni.

Ana zargin Sa’adi ne da wawure wasu kudaden kasar a lokacin da yake jagorantar hukumar kwallon kafar kasar a Libya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.