Isa ga babban shafi
Libya

Libya ta lashi Takobin tsayawa kan Dimokradiyya bayan harbe 'yan Siyasa 2 a kasar

Hukumomi a kasar Libya, sun lashi Takobin tsai da kasar kan tafarkin Dimokradiyya a wani bangare na tabbatar da Doka da Oda bayan harbin da aka yiwa wasu ‘yan Siyasa Biyu a kasar

Wani da aka harbe a Libya
Wani da aka harbe a Libya sbs.com.au
Talla

A ranar Lahadi ne aka ba da Rahoton harbe wasu ‘yan Siyasa daga Jam’iyyar GNC ta kasar tare da jikkata su.

Masu zanga-zanga dauke da Makamai ne suka yiwa Gidan da suke tsinke a birnin Tripoli, a yyainda aka kuma kashe wani Injiniya dan kasar Faransa gabashin birnin Benghazi.

A wata zantawa da aka yi da shi a kafar watsa labarai ta Talabijin shugaban Jam’iyyar GNC Nuri Abu Sahmein, ya ce suna da shirin amincewa da juyin juya halin ran 17 ga watan Fabrairu, domin samar da wanzuwar Dimokradiyya.

Ma’ana yana magana ne akan hargitsin da ya kawar da Gwamnatin shugaba Mu’ammar Ghaddafi.

Abu Sahmein ya ce harin jikkata mambobinsu da ake kaiwa ba zai taba zama babbar barazana a wurinsu ba, sai dai yayi tir da harin.

Yayi kira ga wadancan mafadatan da suka kawar da Gwamnatin Ghaddafi da su yi hubbasar ceton kasar daga halin da ta samu kanta a ciki a halin yanzu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.