Isa ga babban shafi
Libya

‘Yan tawaye sun ba gwamnatin Libya wa’adin Murabus

Wasu tsoffin ‘Yan tawayen Libya daga garin Zintan sun ba Majalisar kasar ta riƙon ƙwarya wa’adin sa’o’I biyar ta yi murabus tare da gargaɗin yin garkuwa da duk Ɗan Majalisar da ya yi watsi da gargaɗinsu.

Ali Zeidan  Firaministan kasar Libya
Ali Zeidan Firaministan kasar Libya REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Wa’adin da Ƴan tawayen suka ba gwamnatin kasar zai kawo ƙarshe ne da misalin ƙarshe 7:30 na dare agogon GMT.

Amma Majalisar kasar ta rikon ƙwarya tace wannan yunƙuri ne na juyin mulki tare da yin watsi da gargaɗin.

A ranar 17 ga watan Fabrairu ne dai mutanen Libya suka yi bikin cika shekaru uku da kawo ƙarshen mulkin Marigayi Kanal Gaddafi. Amma akwai bore da Majalisar ƙasar ke fuskanta bayan sun ƙara wa’adin mulkinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.